Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, yayi magana kan yiwuwar ƙara wa’adin tsofaffin takardun kuɗin naira.
Godwin Emefiele ya bayyana cewa babban bankin ba zai ƙara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin ba daga ranar 31 ga watan Janairun 2023. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Wani matashi ya ƙera jirgi mara matuƙi, bidiyon ya ɗauki hankula
An yi ta kiraye-kirayen ganin an ƙara wa’adin amfani da tsofaffin takardun na naira duba da yadda aka yi ta fuskantar matsaloli.
Da yake magana a gaban kwamitin kuɗi na babban bankin a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, Emefiele ya bayyana cewa:
“Ba ni da labari mai daɗin ji ga waɗanda suke son a sauya wa’adin tsofaffin takardun kuɗi saboda ba zamu ƙara wa’adin ba.”
“Mutane na riƙe naira sannan suna tara ta a gidajen su kuma ba su da hurumin yin hakan, saboda suna yin amfani da hakan wajen yin wasu abubuwa da basu dace ba da naira.”
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu bankin ya karɓi kusan naira tiriliyan ɗaya da rabi N1.5trn, inda yake fatan ya samu naira tiriliyan biyu N2trn kafin nan da cikar wa’adin.
CBN Ya Bayyana Bankuna Biyar Da Zasu Musanya Tsofaffin Kuɗi
A wani labarin na daban kuma, babban bankin Najeriya CBN ya fitar da jerin sunayen wasu bankuna guda biyar waɗanda za suyi musanyar kuɗi.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana sunayen bankuna biyar da zasu shiga cikin tsarin da ya kawo na musayar kuɗi.
Hakan na zuwa ne yayin da wa’adin da aka bayar na daina amfani da tsoffin takardun kuɗi na N200, N500 da N1,000 a matsayin halastattun kuɗi yake ƙara gabatowa.