Sojoji Za Su Fara Fara Fatattakar Yan Ta’addan IPOB – Lagbaja
Babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya umurci dakarun sojin Najeriya da su tabbatar da iko a yankunan da Simon Ekpa yaron Nnamdi Kanu ke bada umarni akai tare da sanya dokar zaman gida, don an tsare shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB a Kudu-maso-Gabas.
Ya yi magana ne kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, Aderemi Adeoye ya tabbatar a jiya cewa rundunar ‘yan sandan jihar za ta ci gaba da samar da tsaro a Anambra musamman ga mutanen da ke son gudanar da sana’arsu ba tare da tsangwama ba, yana mai jaddada cewa ‘yan sanda ba su da wata damuwa da mutanen da suka ce ba zasu fito sana’a ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Za Mu Yi Aiki Da Tinubu Don Tabbatar Da Zaman Lafiyar Yankin Afirka – Shugabannin APC Mazauna Waje
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, Peter Obi, ya bayyana rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas a matsayin ‘ayyukan ta’addanci’.
Ya ce duk da cewa ana alakanta ayyukan da ‘yan asalin Biafra ne, kungiyar da aka haramtawa ta na nesanta kanta daga aikata wadannan miyagun laifuka.
Umurnin Lagbaja na zuwa ne a matsayin martani ga sanarwar da mai fafutukar kafa kasar Biafra mazaunin Finland Simon Ekpa, ya bayar, wanda ya ba da umarnin zaman gida na mako biyu da aka shirya fara yi daga ranar Litinin, 31 ga watan Yuli.
Ekpa ya ce manufar hakan shine neman a gaggauta sakin shugaban kungiyar ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ba tare da wani sharadi ba.
Sai dai mai fafutukar kafa kasar Biafra, ya yi gargadin cewa rashin biyayya ga dokar zaman gida zai haifar da mummunan sakamako.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brigediya-Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana sanarwar ta Ekpa a matsayin haramtacciya data sabawa doka, kuma ya bayyana cewa ba za a amince da hakan ba.
Nwachukwu ya ce an umurci runduna ta 82 ta sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro da su gudanar da sintiri masu karfi, da kuma tabbatar da tsaro, da kuma tabbatar da cewa ‘yan kasar za su iya gudanar da ayyukansu cikin walwala.
A wani labarin kuma:Ka Samar da ma’aikatar kula da harkokin sarakuna – Oluwo ga Tinubu
An bukaci shugaba Bola Tinubu da ya duba batun kafa ma’aikatar harkokin masarautu ta Kasa.
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa da DAILY POST ta samu ranar Alhamis a Osogbo.