Dole Ƴan Najeriya su guji Zaɓen Ruɓaɓɓun Ƴan Siyasa — Cewar Ƴar Takarar Shugaban Ƙasa a NRM
Wata Fitacciyar Farfesa ta Ilmi a Canada kuma ƴar Takarar Shugaban Ƙasa a Najeriya Benedicta Egbo tayi Kira ga ƴan Najeriya dasu guji zaɓar ko sake zaɓen gungun ruɓaɓɓun ƴan siyasa wanda suka sanya ƙasar a wani hali, a lokacin Babban Zaɓen Shekarar 2023.
A cewar ta wannan ya zama dole domin zaɓen sabbin hannu domin su samu nasarar gyara lalata ƙasar da shugabannin da suka gabata suka sanya Ƙasar a ciki.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kori Jami’in Da Ya Cin Zarafin Farar Hula, Yana Karkashin Bincike – NCS
Farfesa Egbo tabayyana haka a ranar Litinin a lokacin da take bayyana ra’ayin ta na yin Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar NRM.
A cewar ta ƴan Najeriya bazasu cigaba da zaɓen mutanen da suka ƙirƙiri matsala ba, kuma suyi tunanin samun canji.
Tace “ƴan siyasar yanzu sun kasa, kuma basu ciyar da Ƙasar a wani mataki ba, inda suka ƙirƙiri matsaloli da suka haɗa da cin hanci da talauci a dalilin matsin Tattalin Arziki.
“Matsalolin dake fuskantar Najeriya ba abune da za’a ɗauke shi da wasa ba, domin Ƙasar tana da dukkanin masu ilmi da Albarkatu da dukkanin abinda ake buƙata. A takaice Najeriya na iya zama Ƙasar da zata zamanto waɗanda suka yi fice kuma wadda ake girmamawa a faɗin Duniya.
“Amma ana buƙatar Shuwagabanni masu hangen nesa, masu zuciyar cigaba, masu kishi wanda ke kallon makomar ƙasar.