Gwamnatin Tarayya ta dage kan cewa ya kamata ‘yan Najeriya su tashi tsaye domin karin farashin mai, saboda taɓarɓarewar tattalin arzikin da kasar ke ciki.
Ministan ya ce, “Abin takaici ne matuka idan har akwai kari a farashin famfon mai, amma idan ya zama babu wata mafita sai an ƙara kuɗin man ya kamata ƴan Nijeriya su yi haƙuri su karɓa domin hakan na da nasaba da matsalar tattalin Arziƙin da ake ciki.
“Shin za mu iya ci gaba da tallafawa tallafin da ba lallai ne talaka ya amfana da shi ba, amma yana amfanar wasu daidaikun mutane‘ yan kasuwa a kasar nan Ba na so in tantance mutanen da ke cin gajiyar wannan Tallafi amma dai ba talaka a cikin su.
“Tallafi baya amfanar yan Najeriya kai tsaye; babbar huldar da ‘yan Najeriya ke amfana da ita a ɓangaren mai shine shan kananzir wanda mutane ke amfani dashi wajen girki; kamar man dizal, ana amfani da shi ne wajen jigilar kayan abinci da sauransu. Amma wadannan an dade ba su da tsari.
Dan haka madadin a riƙa bayar da tallafin wasu na cinyewa gwara a ƙara kuɗin man a cire tallafin kowa ya huta.