Sojoji a Kasar Cote de Ivoire sun chafke mutane da dama a birnin Abidjan cibiyar kasuwancin kasar, sakamakon zargin au da hannu dumu-dumu kan harin da aka kai wani matsugunin sojin a ranar Litinin.
An kama mutanen sha biyu ne biyo bayan wani bayanan sirri da jami’an tsaron Gendarmerie suka tattaro karkashin umarnin Ma’aikatar tsaron kasar.
A ranar 21 ga watan da muke ciki na Afirelu nw dai wasu yan bindiga suka farmaki matsugunin sojin dake N’dotre na Arewacin Abidjan.
A sa’ilin harin an jikkata wani jami’in soji guda yayin da aka hallaka uku daga maharan sai kuma aka jikkata hudu daga cikin su.
Mahukunta a kasar sun ce an samu Fasfo a na kasar Laberiya a jikin biyu daga maharan inda kuma ana chana ana ci gaba da gudanar da bincike.
To sai dai kasar ta Laberiya ta yi Allah wadai da harin, inda kuma ta yi alkawarin inganta tsaro a yankin ta.
Da ma dai masana harkokin tsaro sun sha gargadin cewa muddin ba a tashi tsaye ba to lallai aikin masu Ikirarin Jihadi da ya fara a arewacin Mali a shekara ta 2012 ka iya bazama zuwa wasu sassan nahiyar Afirka.