Dole a maida yara su riƙa zuwa makaranta – Minista
Karamin Ministan Ilimi, Yusuf Sununu, a ranar Laraba a Yola, ya ce gwamnatin tarayya ta kara zage damtse wajen ganin an dawo da yaran da ba su zuwa makaranta don ci gaba da karatu a makarantu.
Ministan, wanda ya bayyana haka a wajen kaddamar da yaki kan yaran da ba sa zuwa makaranta a shekarar 2024 na shiyyoyi hudu na Najeriya, ya ce an yi hakan ne domin a samu ingantacciyar al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN:NUT, NULGE: Wike ya ƙulla yarjejeniya da malaman makarantun Abuja da ke yajin aiki
Mista Sununu wanda ya samu wakilcin Joy Onoja, mataimakin darakta a ma’aikatar ilimi ta tarayya, ya ce har yanzu ana tauye wa kananan yara ‘yan kasa hakkinsu na ilimi.
“Batun zamantakewa da al’adu da tattalin arziki masu rikitarwa da duniya ke fama da cutar ta COVID-19 sun kara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
“Tsarin taswirar fannin ilimin Najeriya don sabunta bege na 2023 zuwa 2027 ya kuma lura cewa har yanzu kasar tana da mafi yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.
“Wannan shine dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta himmatu ba tare da gajiyawa ba wajen samar da yanayin da kowane yaro zai samu damar koyo, girma da bayar da gudummawa mai ma’ana ga al’umma.”
Ya kuma ba da tabbacin cewa ma’aikatar za ta zakulo irin wadannan yaran, tare da tabbatar da an shigar da su a cibiyoyin koyo na yau da kullun da kuma wadanda ba na yau da kullun na kusa da gidajensu tare da samar da kayan makaranta don ci gaba da koyo.
Malam Sununu ya bukaci masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni da jama’a da su hada kai tare da tabbatar da an baiwa yara marasa galihu tallafi da daukar nauyin sana’o’i daban-daban domin a samu amintacciyar al’umma.
Shima da yake nasa jawabin kwamishinan ilimi na jihar Adamawa Dr Umar Pella ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na ganin kowane yaro a jihar ya samu ilimi.
A wani labarin kuma:Ƴan sanda sun kama wani mai garkuwa da mutane a Abuja
Rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja a ranar Larabar da ta gabata ta ce ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne yayin da rundunar ta musamman ta ke daukar karin matakai na kare mazauna yankin.
Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da babban birnin tarayya Abuja Haruna Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.