Dole ne mu hukunta masu garkuwa da mutane kamar ƴan ta’adda – Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da yawaitar sace-sacen mutane a fadin kasar, inda ya bayyana cewa dole ne a dauki mutanen da ke da hannu a matsayin ‘yan ta’adda.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Talata a liyafar cin abinci na watan Ramadan tare da mambobin ma’aikatan shari’a na tarayya, karkashin jagorancin babban jojin Najeriya (CJN), Mai shari’a Olukayode Ariwoola.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dangote ya ƙaddamar da rabawa Al’umma tallafin kayayyakin abincin Naira Biliyan 15
“Dole ne mu dauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda. Matsorata ne,” in ji shugaban.
“A wulakanta su. Suna zuwa makarantu suna sace yara suna haifar da rashin jituwa.
“Dole ne mu dauki su daidai a matsayin ‘yan ta’adda domin mu kawar da su, kuma na yi muku alkawarin za mu kawar da su.”
liyafar cin abincin ta samu halartar jami’an shari’a masu yiwa kasa hidima da masu ritaya, da suka hada da tsoffin manyan CJN guda biyu, Mai shari’a Mahmud Mohammed da Justice Walter Onnoghen.
A wani labarin kuma:Harin Mairua: Gwamnan Katsina zai tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya yi Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a garin Mairua da ke karamar hukumar Faskari a jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin tausayi.
Harin wanda ya afku a yammacin ranar Asabar din da ta gabata a lokacin sallar magariba a watan Ramadan da muke ciki, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu biyu.