Harin Mairua: Gwamnan Katsina zai tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya yi Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a garin Mairua da ke karamar hukumar Faskari a jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin tausayi.
Harin wanda ya afku a yammacin ranar Asabar din da ta gabata a lokacin sallar magariba a watan Ramadan da muke ciki, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kada ku karɓi kuɗin tafiya aikin Hajjin ku – An gargaɗi mahajjata
Gwamna Radda, ta bakin sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari ya yi Allah wadai da harin tare da jajantawa. Ya kuma yi alkawarin tallafa wa iyalan wadanda suka rasu, sannan ya bukaci mazauna yankin da su yi addu’ar Allah ya dawo da matar da ‘yarsa da aka sace. Ya kuma yi addu’ar Allah ya dawo da shi yankin lafiya.
Alhaji Lado Mairuwa, babban manomi kuma dan kasuwa ne ya bayar da kyautar koli a yayin harin. Marigayi Lado ya bar mata hudu da ‘ya’ya 26, yayin da makwabcinsa, Sani Abdullahi wanda shi ma aka kashe a lokacin da yake kokarin taimakon marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 20.
Domin kara ta’azzara matsalolin iyalai, ‘yan fashin sun sace matar marigayin, Hajia Rabi, da diyarsa mai shekaru 14, Maryam. Har yanzu ba a san inda suke ba.
A yayin ziyarar ta’aziyyar dan marigayin Umar Abdulhamid mai shekaru 18, wanda lamarin ya faru a gaban idonsa ya ce ‘yan bindigar sun harbe mahaifin nasa ne bayan ya bijirewa yunkurinsu na dauke shi. Ya kuma tabbatar da cewa, wani makwabcinsu Sani Abdullahi da ya zo taimako shi ma ‘yan bindigar sun harbe shi har lahira.
Yayin da suke yaba da damuwar gwamnan da kuma kokarin gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro, mazauna garin Mairuwa sun roki gwamnatin tarayya da ta dauki kwakkwaran mataki. Sun kuma yi kira da a kara tsaurara matakan tsaro a jihar Katsina da makwabta kamar Zamfara da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
A wani labarin kuma:Dangote ya ƙaddamar da rabawa Al’umma tallafin kayayyakin abincin Naira Biliyan 15
Wata kungiyar farar hula, CSO, da ke mai da hankali kan al’amuran Hajji da Umrah, kungiyar masu rajin aikin Hajji mai zaman kanta, IHR, ta yi kira ga dukkan maniyyata aikin Hajji na 2024 da kada su yi gaggawar karbar kudaden ajiya daga hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi.
Shawarar dai ta biyo bayan matakin da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta dauka na neman dukkan maniyyatan da suka biya kudin farko na Naira miliyan 4.9 da su biya karin Naira miliyan 1.9 kafin ranar 28 ga Maris, 2024.