Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, FRSC reshen jihar Akwa Ibom, za ta rarraba jami’anta 687 a fadin jihar domin lura da zirga-zirga a lokacin bukin Easter.
Mr Oga Ocho, Kwamandan FRSC na jihar shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa day a fitar a ranar Laraba a garin Uyo, inda ya gargadi direbobi akan da su guji guje-guje mara ka’ida da kuma halayen da ba su dace ba akan tituna.
Ochi har wala yau ya nemi jami’ai na musamman da aka rarraba domin lura da bukin Easter din da su tabbata da masu amfani da titunan sun bi ka’idodin amfani da tituna domin gujewa hadurra.
Ya tunatar da su cewa a lokacin bukukuwa irin an Easter masu amfani da titunan na kara karuwa ne, inda ya nemi da su sanya ido sosai akan yadda za a yi zirga-zirga a lokutan bukin.
Ya kuma shawarci matuka da su guji tuki cikin shaye-shaye. Sannan su yi amfani da dokokin kariya da cutar korona domin dakile yaduwar cutar a fadin kasar.