Tsohon Shugaban Ƙasar Amurka Donalad Trump ya miƙa wuya ba tare da nuna turjiya ba bayan bayan tsare shi na ɗan lokaci da aka yi a jihar Georgia.
Ana yiwa Trump shari’a ne bisa zargin yunƙurin sauya sakamakon zaɓen jihar a 2020, wanda ana ganin shi ne a karon farko da irin haka ta faru da wani tsohon shugaban ƙasar Amurka.
KARANTA WQNNAN LABARIN: Ni Nake Hana Sojojin ECOWAS Afkawa Kasar Nijar–Tinubu
Tsohon shugaban zai biya dala 200,000 a matsayin kuɗin beli kafin sakinsa daga gidan kason na birnin Atlanta inda aka tsare shi na ɗan lokaci domin jiran yanke masa hukunci.
Daga baya dai Trump ya bayyana shari’ar da ake masa a matsayin “cin amana”.
Ana ganin shi ne karo na huɗu da ake tsare Trump cikin wata biyar a jere a bisa zarginsa da aikata manyan laifuka.
Toh sai dai kuma wannan ne karon farko da jami’an ‘yan sanda suka bayyana hotonsa.
Tsohon shugaban ƙasar rabon da ya wallafa wani abu a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter baya tun watan Janairun 2021.
Amma a wannan karon ya wallafa a shafin nasa cewar: “Kutse a sha’anin zaɓe. Ba gudu ba ja da baya!”.
Yanzu dai shugaba Trump ya shiga sahun fitattun Amurkawa da aka tsare su ta wannan hanya, waɗanda suka hada da Elvis da Frank Sinatra da Al Capone da kuma Dakta Martin Luther King.
A makon da ya gabata ne aka gurfanar da Mista Trump shi da wasu mutane 18 dake kareshi bisa zargin hargitsa zaɓen Jihar Georgia bayan da ya yi rashin nasara da kuri’a 12,000 a hannun shugaba mai ci Joe Biden.