Hukumar kula da gidan gyaran hali da tarbiyya ta Najeriya reshen jihar Legas ta tabbatar a ranar Asabar cewa gwamnatin jihar Legas ta yi afuwa tare da sakin fursunoni 30.
Kakakin hukumar NCoS a Legas, Mista Rotomi Oladokun ne ya tabbatar da sakin a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Legas.
KARANTA WANNAN: Wani Gwamna a Arewa Ya Bayar Da Umarnin Dakatar Da Shirin Nada Basaraken Gargajiya
Oladokun ya bayyana cewa babban alkalin jihar, Mai shari’a Kazeem Alogba ne ya yi wa fursunonin afuwa.
“Fursunonin da aka saki su ne wadanda suka aikata kananan laifuffuka kamar cin zarafi, haifar da rashin tsaro, satar kananan kaya, laifukan ababen hawa da dai sauransu.
“Akwai bukatar a sake ‘yantar da wasu fursunonin saboda wuraren da ake tsare da su na jihar na dauke da fursunoni sama da 8000, wanda adadin ya fi karfin wajen,” in ji Oladokun.
Oladokun ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi amfani da tsarinta na shari’a wajen duba bayanan fursunonin don ganin ko za a iya sakin wasu fursunonin nan gaba.
Bugu da kari ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su karbi fursunonin da aka sako su kuma taimaka musu su dawo yin rayuwa cikin al’umma.
(NAN)
A wani labarin kuma, Adamawa: Binani Ta Maida Martani Kan Tsaiko Da INEC Ke Shirin Kawo Wa Ga Shari’ar Ta
‘Yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben gwamna da ya gabata a jihar Adamawa, Sanata Aishat Dahiru Binani, ta zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da rashin cika ka’idojin da ta shigar na kin bayyana Adamu Fintri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Binani ta yi zargin cewa hukumar zaben, a wani mataki na nuna son zuciya da rashin bin umarnin kotu, a yanzu haka tana kokarin kamawa tare da tsare kwamishinan zaben da aka dakatar, Barista Hudu Yunusa Ari a matsayin wata dabara ta hana shi shaida a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa da ke ci gaba da gudana.