Gwamnatin jihar Legas ta ce kawo mutane kimanin dubu dari da ashirin da bakwai da dari takwas da tamanin da biyar ne suka samu yin rigafin annobar Covid-19 na Kamfanin AstraZeneca.
Kwamishinan Lafiyar Jihar Akin Abayomi shine ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.
Abayomi ya ce rahoton Hukumar Lafiya matakin farko ya nuna cewa a kwanaki goman farko da ta gudanar da rigafin, ma’aikatan jinya dubu talatin da tara da dari tara da hamsin da tara, sai Ma’aikata gwamnati dubu hamsin da hudu da dari da kuma masu rike da manyan mukamai ne suka samu karɓar rigafin.Kwamishinan ya ce Wannan alkaluma ya sa Jihar Legas ta fi ko wace Jiha yin wannan rigafi ciki har da birnin tarayya Abuja.
Ya kara da cewa a yayin rigafin, alkaluman sun nuna cewa mata ne suka fi rinjayar rigafin fiye da maza.