Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a ranar Litinin ta ce ta sake kama fitaccen jarumin nan na dandalin sada zumunta Ismaila Mustapha, wanda aka fi sani da Mompha, wanda tun farko aka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin almundahanar kudi har naira biliyan shida. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Lauyan hukumar EFCC Suleiman Suleiman ya shaida wa wata kotun hukunta laifuka da ke zama a Ikeja na jihar Legas cewa, masu gabatar da kara tare da hadin gwiwar abokan huldar ta na kasa da kasa sun samu nasarar cafke Mompha.
KARANTA WANNAN LABARIN: An bayyana Alkalin Wasan Da Zai Hura Karawar Man City Da Real Madrid
Daga nan mai shari’a Mojisola Dada ta dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 3 ga watan Yulin shekarar 2023.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa kotun ta bayar da umarnin ne a ranar 21 ga watan Satumban shekarar 2022, lokacin da ta fara shari’ar wanda ake tuhuma ba ya nan bayan ya kasa bayyana a gaban kotu.
A ranar 22 ga watan Junairu, 2022, EFCC ta gurfanar da Mompha a gaban kuliya tare da kamfaninsa Ismalob Global Investment, a kan tuhumar da ake masa na karkatar da Naira biliyan 6, inda ya ki amsa laifinsa.
Kotu a ranar 22 ga Yunin shekarar 2022, ta bayar da sammacin kama Mompha bayan rashin zuwansa kotu. Dada ta soke belin da ta ba wanda ake tuhuma.
A wani labarin kuma, Mai Rabon Ganin Badi: Guda Daga Cikin Yammatan Chibok ta tsere daga Hannun Boko Haram
Sojojin Najeriya sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok, Saratu Dauda, wacce ta kubuta daga hannun ‘yan ta’adda a dajin Sambisa na jihar Borno. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kwamandan rubdunar Operation Hadin Kai, ManjoJanar Ibrahim Ali, ya ce sojojin sun, ceto Saratu mai shekaru 25 a ranar 6 ga Mayun shekarar 2023.