Sojojin Najeriya sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok, Saratu Dauda, wacce ta kubuta daga hannun ‘yan ta’adda a dajin Sambisa na jihar Borno. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kwamandan rubdunar Operation Hadin Kai, ManjoJanar Ibrahim Ali, ya ce sojojin sun, ceto Saratu mai shekaru 25 a ranar 6 ga Mayun shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: An bayyana Alkalin Wasan Da Zai Hura Karawar Man City Da Real Madrid
Yayin da yake mika ta ga kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Zuwaira Gambo, a ranar Litinin a Maiduguri, Janar Ali, ya bayyana cewa Saratu Dauda ta auri wani Abu Yusuf wani kwararre kan sarrafa abubuwan fashewa acikin mayakan Boko Haram.
Ya kuma kara da cewa wadda aka sace tana da ‘ya’ya uku tare da mijinta da aka tilasta mata ta aure shi, amma ta bar su acan yayin da ta samu hanyar gudu.
A halin da ake ciki, kwamandan sojojin ya ce ana ci gaba da kokarin ceto yaran da Saratu Dauda ta haifa daga hannun mijinta.
Hakan ya faru ne kamar yadda ya bayyana cewa an kai ta asibitin sojoji na Maimalari domin samun kulawa ta musamman kafin mika ta ga gwamnatin jihar.
Janar Ali ya ce ya zuwa yanzu ‘yan matan makarantar Chibok 76 ne suka tsere daga hannun yan ta’addan, yayin da Boko Haram suka sako 107 a shekarar 2018 daga cikin 276 da aka sace a ranar 14 ga Afrilun sgekarar 2014.
A cewarsa, ‘yan matan makaranta 186 ne Sojoji suka ceto, yayin da har yanzu 93 ke channun ‘yan ta’addan.
Ya kara da cewa a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023, sojojin sun ceto ‘yan matan makarantar Chibok 19, ciki har da 11 a bara.
Sai dai Gambo ta shaida wa manema labarai cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kammala karatunsu na sakandare da jami’a a jihar.
Kwamishiniyar ta kara da cewa za a kai ta cibiyar koyon sana’o’i da ke Maiduguri domin shiga cikin wasu da a halin yanzu suke samun horon dogaro da kai domin amfanar al’umma.
A wani labarin kuma, Shugabannin kasashe 120 Na Sha’awar Halartar Bikin Rantsar Da Tinubu – Jigon APC
Adamu Garba, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, ya ce sama da shugabanni 120 ne suka nuna sha’awarsu ta halartar bikin rantsar da zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar 29 ga Mayu, 2023. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a gidan talabijin na Arise a ranar Litinin.