Duk Da Najeriya Na Da Girma, Ni Ba Za Ta Yi Man Wahalar Sarrafa Ta Ba – Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce aikin kiyaye Najeriya a matsayin ƙasa daya ne shine a gabansa, yana mai jaddada cewa kalubalen da ke ci gaba da cusa al’ummar kasar nan cikin mawuyacin hali na wucin gadi ne.
Da yake magana a yayin gabatar da wani littafi mai suna “Brutally Frank”, wanda tsohon ministan yada labarai, Edwin Clark ya rubuta a ranar Alhamis a Abuja, Tinubu ya ce Najeriya na da sarkakiya, amma ba ta da wahalar iya sarrafa wa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Mun Cire Tallafi Ne Saboda Gyaran Goben Ku – Tinubu Ga Ƴan Najeriya
Shugaban wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume ya wakilta, ya ce, “Don ci gaba da rike Najeriya aiki ne da ya kamata a yi.
“Wannan kasa tana da sarkakiya, amma ba za ta taba zama da wahala a iya sarrafa ta ba. Al’adunmu da addininmu daban-daban sun zama tushen ƙarfinmu.”
Shugaban ya ce radadin da ake fama da shi a halin yanzu sakamakon cire tallafin man fetur na wucin gadi ne, yana mai jaddada cewa nan ba da jimawa ba zai tafi tare da kawar da abubuwan jin dadi.
Sarkin Kano Ado Bayero ya ce, “Muna da kalubale da dama; yawan hawa da sauka.
Ya kamata shugabanninmu su yi amfani da hikimar da suke da ita wajen ganin kasar nan ta dunkule wuri daya domin mu samu sauki daga kalubalen da muke fuskanta.”
A nasa jawabin, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yabawa Clark, inda ya ce ya rubuta sunansa da zinare saboda irin gudunmawar da ya bayar da kuma gwagwarmayar ganin an samu dunkulewar kasa tare da zaman lafiya.
Shugaban taron kuma tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (rtd) ya ce, “Ina fatan matasa za su samu karin bayani kan abubuwan da suka faru da su wanda ya kawo kasar nan halin da take ciki a yau, wanda shugaban kasarmu a kai.
A wani labarin kuma:Rashin Tsaro A Najeriya Na Matukar Tayar Min Da Hankali-Peter Obi
Dan wasan gaba na Inter Miami Lionel Messi ya ce komawarsa zuwa Major League Soccer (MLS) shine canja kulob ɗinsa daga “kishiyar” kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona zuwa Paris Saint-Germain.
Messi ya rattaba hannu a kulob din MLS bayan ya shafe shekaru biyu a Faransa tare da PSG.