“Ka Magance yunwa a Jihar ka” ~ APC ga Gwamna Makinde
Jam’iyyar APC a Jihar Oyo ta gargadi Gwamnan Jihar Seyi Makinde na Jam’iyyar PDP da ya magance yunwar da al’ummar Jihar ke fama da ita.
Gargaɗin ya biyo bayan amincewa da wata kwangila da Gwamnan yayi wacce za ta laƙume maƙudan kuɗaɗe baya ga halin matsi da yunwa da al’ummar suke ciki, inda suka bukaci da ya magance yunwa maimakon Wannan.
Da suke tsokaci dangane da sanarwar da Gwamnatin Jihar ta fitar cewa ta amince da Naira biliyan 3.35 don siyan motocin Kia Rio a matsayin motocin tsaro da kuma wasu Naira biliyan 3.19 don kula da fitilun tituna a Jihar, Jam’iyyar ta bayyana hakan a matsayin kashe kuɗi ba inda ya dace ba.
Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta Olawale Sadare ya fitar ta ce, a matsayin su na masu ruwa da tsaki a Jihar, ba za su rungume hannu suna kallon Gwamnan na Jam’iyyar PDP yana kashe kuɗaɗen jihar ba bisa ka’ida ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rashin Tsaro A Najeriya Na Matukar Tayar Min Da Hankali-Peter Obi
Sanarwar ta kuma ƙalubalenci Gwamnan akan kashe biliyoyin Naira wajen siyan motocin alfarma na Kia Rio a matsayin motocin jami’an tsaro inda ta bayyana cewa a shekarun baya ma anyi irin haka, wanda a halin yanzu ƴan kaɗan ne daga cikin motocin ake gani yayin da mafi yawancin su suka yi ɓatan dabo.
Yanzu haka dai Gwamnatin Jihar ta sake maimaita wannan aika-aikar inda ta amince da Naira biliyan 3.35 a kan motocin tsaron guda 105.
Baya ga cewa irin waɗannan motocin ba an siyo su ba ne don fita rangadin neman masu laifi, sai ma farashin kowace mota ya kai Naira Miliyan 32 kuma wannan abu ne da ba za a amince da shi ba inji APC
Haka kuma a kan batun Naira biliyan 3.19 da aka amince da shi na kula da aikin fitilun tituna wanda za a kashe sama da Naira biliyan 28 da za a aiwatar ba tare da bin ka’ida ba mun yi kakkausar suka akan haka, domin babu hujjar kashe makudan kudade wajen maye gurbin sanduna fitilun ba kaɗai, suna mai cewa hakan bai dace ba.
A maimakon buɗe wata hanya ga wasu masu hannu da shuni da ke kewaye da Gwamnati na wawushe dukiyar al’umma, kamata yayi Gwamna Makinde ya yi koyi da wasu gwamnoni da suka yi kokari sosai a ‘yan kwanakin nan wajen tunkarar kalubalen da ake fuskanta a jihohinsu.
Ya kuma kamata ya magance matsalolin ma’aikata da ’yan fansho a Jihar da suka ajiye aiki a kwanakin baya suna masu kokawa dangane da yadda ake tafka magudi da yaudara a harkar biyan fansho daga Gwamnatin PDP tun daga shekarar 2019.