Wata matar aure tayi ƙorafin cewa mijinta baya ganin ƙimar auren su saboda wasu abubuwa da yake mata.
Ta bayyana cewa mijinta yana biyanta kuɗi duk lokacin da suka yi kwanciyar aure, sannan kuma yana kai ta zuwa otal daban-daban inda yake bata kuɗi duk lokacin da suka goge raini akan gado. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: PDP na shirin ɗauko hayar ƴan baranda domin murde zaben ranar Asabar a Katsina – APC
Matar ta bayyana cewa tana matuƙar jin ciwon abinda mijin nata yake yi mata domin a tunanin ta baya ganin ƙimar ta kwata-kwata, domin abinda yake mata yana sanyawa tana jin kamar yana ɗaukar ta a matsayin mai raba albarkatun jikin ta a bakin titi.
Matar ta bayyana cewa lokacin da suke soyayya, tayi tunanin cewa abu ne mai kyau saurayin ta ya riƙa bata kuɗi bayan sun biyawa juna buƙata.
Matsalar ta yanzu shine duk da cewa auren su ya kai shekara uku, har yanzu yana biyanta duk lokacin da suka goge raini akan gado.
Tayi bayyana cewa har yanzu basu taɓa samun haihuwa ba, sannan tayi tunanin cewa tun da sun zama miji da mata wannan ɗabi’ar tasa zata sauya.
Ga bidiyon nan ƙasa:
Magidanci Na Son Ƙara Aure, Zai Biya N500k Kuɗin Sadaki
Wani magidanci mai shekara 57 a duniya wanda ya fito daga jihar Kaduna yana neman ƙara aure inda zai auri mace ta biyu.
Shafin haɗa aure na Halal matchmaking a Twitter shine ya bayyana abubuwan da magidanci yake buƙata a wajen duk wacce ta shirya zata aure shi.