Gwamnan jahar Borno, baya goyon bayan ko wane bangare kan kafa sabbin masarautu a kano.
Ina da alaka mai kyau tsakanin su biyun duka Ganduje da sarki.
Ya kara da cewa bana goyon bayan Gwamna kan wanann rabo da yayi haka zalika bana goyon bayan sarki Muhammad Sunusi na biyu.
Shattima yana wanann jawabi ne a gaban manema labarai a kaduna yayin da suke taron gwamnoni.
Ganduje ya dau marayu Dari biyu 200 ‘Yan gudun hijra Wanda bazan mantaba.
Sarki kuma shine ya fara hada ni da Dangote a 2016 inda har Dangote yaje Borno, har Sau uku kan halin da aka tsinci kai a baya.
Kaga kowa nawa ne a cewar sa.