Wakilinmu Adamu A. Albarkawa
Kutaren da ke kauyen alheri a garin ‘yangoji, a karamar hukumar kwali dake babban Birnin taryya Abuja, sun nuna damuwar su, bisa gudumawar da suka baiwa shugaban kasa Muhammad Buhari Wanda hakan ya yi jagorancin samun nasarar shi a shekara ta 2015 da kuma zaben da aka yi a farkon wannan shekarar amma kawo yanzu basu taba amfana da komai ba daga Gwamnatin sa.
Jagoran kauyen Alh. isa, ne ya furta hakan a ranar Asabariyar nan lokacin da yake karban kayyakin abinci da kungiyar bada tallafi ta Qatari ta tallafa masu.
Alh. isa ya koka matuka bisa yadda garinsu ya kasance babu wutar a kusan shekaru shidan da suka wuce, sakamakon sace masu nau’rar Samar da lantarkin su da wasu marasa kishin kasa su ka yi awon gaba da shi, Wanda sakamakon matsanancin duhun da suka shiga macizai da kwankwamai na matukar damun mazauna kauyen.
Har-wa-yau ya koka matuka game da rashin Magunguna a cibiyar shan maganin da gwamnati ta Samar masu, ya kuma kara da cewar hatta takin zamanin da za su sanya a gonakin su lamarin ya ci tura.
Ali daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta kai masu dauki ta hanyar Samar masu da kayyakin more rayuwa.
Ya kara da cewar abun kunya ne ace har sai irin wadan nan kungiyoyi masu bada tallafi na duniya sun tallafa masu a daidai lokacin da gwamnati ta juya masu baya.