Wani binciken masana ya bayyana sauyin yanayi a matsayin babbar matsalar da ke haifar da tashe-tashen hankula da kuma rashin hadin ka tsakanin al’ummomi, bayan kwashe dogon lokaci ana fama da rikici a Somaliya.
Binciken da Cibiyar Wanzar da Zaman Lafiya ta Stockholm ta gudanar, ya yi nazari kan rawar da ofishin Majalisar Dinkin Duniya ke takawa a Somalia da kuma illar da sauyin yanayi ke yi, in da ya yanke hukuncin cewar matsalar na matukar tasiri wajen haifar da rigingimu.
Florian Krampe, babbar mai bincike a cibiyar ta ce, matsalar fari ta zafafa rikicin Somalia ganin yadda aka kwashe dogon lokaci ana fama da karancin ruwan sama.
Binciken ya ce, fari da ambaliya sun tilasta wa dubban mutane barin matsugunansu zuwa sansanonin da ake dibar su wajen shiga ayyukan ta’addanci.