By Abbas Yakubu Yaura
Sabon kwamishinan ‘yan sanda, CP Edward Chuka Egbuka, ya fara aiki a matsayin kwamishinan ‘yan sanda na 36 na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi.
Hakan ya biyo bayan sauya CP Idrisu Dauda Dabban ne zuwa shelkwatar rundunar ‘yan a matsayin kwamishinan sadarwa na ‘yan sanda.
Wata sanarwa da CZ:5300/KGS/PPRO/Vol.T/128 da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP William Aya, ya fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa an shigar da CP Egbuka aikin ‘yan sanda ne a ranar 15 ga Maris, na shekarar 1988 a matsayin mataimakin Sufeto na Cadet, ya samu horo a Makarantar ‘Yan sanda ta Annex dake Jihar Kaduna.
Sannan yace “Shi gogaggen jami’in dan sanda ne na kasa-da-kasa wanda ya tsaya tsayin daka na aiwatar da doka da aikin ‘yan sanda tare da gogewar wanzar da zaman lafiya ta duniya.
Sannan yace “Shi mamba ne na kungiyar shugabannin ‘yan sanda ta duniya. Ya halarci kwasa-kwasan Tactical and Leadership a ciki da wajen Najeriya. Daga shekarar 1994-1995, sannan ya kasance a Majalisar Dinkin Duniya a matsayin jami’in ‘yan sandan farar hula a Ruwanda, Gabashin Afirka,” in ji sanarwar.
“CP Egbuka ya yi ayyuka da dama a cikin rundunar har da tsohon kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ‘yan sandan jihar Filato.
“Ya kuma yi aiki a matsayin kwamishinan ayyuka na ‘yan sanda a hedikwatar rundunar. Har zuwa wannan lokacin, shi ne kwamishinan ‘yan sanda mai kula da harkokin sadarwa a hedikwatar rundunar da ke Abuja.
“A matsayinsa na mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, ya taba rike mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka na rundunar ‘yan sandan jihar Osun da na jihar Kogi da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da binciken manyan laifuka a shiyya ta 7, dake hedkwatar Abuja.
“Sabon Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma yi aiki a matsayin Kwamandan yankin a Ogba, Legas, Idimu, Legas, Umuahia, Jihar Abia, da kuma sashen Lantang dake Jihar Filato.
“CP Egbuka ya yi aiki a matsayin mataimakin sakataren rundunar a hedikwatar rundunar da ke Abuja da kuma jami’in ‘yan sanda na shiyyar sassa daban-daban a fadin tarayya.
Comments 1