Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gayyaci ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci, Betta Edu da aka dakatar zuwa hedikwatarta da ke Abuja, domin amsa tambayoyi.
Hakan ya biyo bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi mata daga ofis bisa zargin biyan tallafin naira miliyan 585.189 da ake cece-kuce.
Karanta nanNayi Danasanin Zaben Fubara A Matsayin Wanda Zai Gajeni-Wike
Ku tuna cewa a ranar Litinin ne shugaba Tinubu ya dakatar da Edu daga mukaminta ba tare da bata lokaci ba, sannan ya umarci hukumar EFCC da ta binciki ayyukan ma’aikatar agaji da yaki da fatara.
Tinubu ya yanke shawarar ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar.
Ko da yake mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, bai amsa kiransa ba ko kuma ya tabbatar da labarin, wasu majiyoyi masu inganci sun shaida wa LEADERSHIP jim kadan bayan dakatarwar da aka yi cewa gayyatar ta zo kasa da mintuna 30 bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da dakatar da Edu daga ofis.
Majiyar ta kuma bayyana cewa tun da farko hukumar EFCC ta bada shawarar dakatar da ministar domin share fagen gudanar da cikakken bincike kan harkokin ma’aikatar.
A wani labarin kumaBa Daga Wajenmu Jadawalin Farfesoshin Bogi Ya Fito Ba-NUC
Majiyar ta bayyana cewa hukumar ta fara aiki ne bayan da shugaban kasar ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan batun biyan tallafin naira miliyan 585.189 da ake cece-kuce.
Daya daga cikin majiyoyin EFCC ta ce binciken da muke yi kan zargin biyan ba zai tafi daidai ba idan ba mu ba da shawarar dakatar da Ministar ba,dakatar da ta zai ba mu ’yancin yin aikinmu sosai kamar yadda shugaban kasa ya umarce mu.
Tuni aka aike mata da takardar gayyata a hukumance muna tsammanin za ta girmama gayyatar don ba da haske mai kyau game da batun da ake zarginta,don haka, muna sa ran ta zo nan ba da jimawa ba.