Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta musanta rahoton da ke yawo a yanar gizo cewa ta bankado jimillar Farfesa 100 na jabu a wasu jami’o’in kasar nan.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren hukumar, Chris Maiyaki.
Karanta nanDa dumi-dumi: Kotun koli ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara kan zaɓen Ebonyi
Ya ce duk da cewa ta fara tantancewa a shekarar 2019 ga malaman jami’o’in Najeriya, ko kadan ba ta fitar da jerin sunayen Farfesa na bogi ba a shekarar 2024.
Don kauce wa shakku, hukumar za ta iya tabbatar da cewa a shekarar 2019 ta fara wani aiki da za a yaba, da niyyar hadawa da kuma buga jerin cikakkun Farfesa a cikin Tsarin Jami’o’in Najeriya ta hanyar amfani da tashar yanar gizo don tattara bayanan da ake bukata.
A lokacin wannan aikin NUC ta sami abubuwan da ba su da kyau, kamar su Farfesoshin bogi da aka jera a matsayin cikakkun Farfesoshi.
Yana da muhimmanci a kuma bayyana a fili cewa Hukumar a matsayinta na Hukumar Gwamnatin Tarayya, ba ta gudanar da atisayen da za su iya bata sunan Najeriya da NUS.
A wani labarin kumaYanzu-Yanzu: Da Yuwuwar Kotun koli Ta Yanke Hukunci A Shari’ar Zaben Kano Da Wasu….
Don haka ne hukumar ta ga ya dace ta raba bayanan da aka tattara ga jami’o’in Najeriya domin tantancewa daga hukumomin da suka dace kan wanda ya cancanci zama cikakken farfesa,” a cewar sanarwar hukumar.
LEADERSHIP ta tuna cewa rahoton na bogi ya tilastawa kusan daukacin jami’o’in da aka ambata yin watsi da samuwar Farfesa na jabu a ma’aikatansu.