Hukumar hana cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC, ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake a Zaria gaban kotu.
An gurfanar da Farfesa Ibrahim Garba tare da Ibrahim Shehu Usman, ma’ajin kuɗi na jami’ar a gaban wata babban kotun jihar Kaduna a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairun 2023. Rahoton jaridar Legit.ng ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Yadda aka yiwa wata mata fyaɗe a gaban ƴar ta mai shekara biyu a duniya
Hukumar EFCC a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu, tace ta gurfanar da su a gaban kotun bisa zarge-zargen da ake musu akan laifuka 8 da almundahanar kuɗi waɗanda za su kai naira biliyan ɗaya.
An cafke tsohon shugaban jami’ar tare da ma’ajin ne bayan shigar da ƙorafe-ƙorafe akan su.
Hukumar tace jami’anta sun gudanar da bincike cikin tsanaki na watanni bayan an shigar ƙorafin cewa waɗanda ake zargin sun karkata akalar maƙudan kuɗaɗe.
Kuɗaɗen a cewar EFCC, an ware su ne domin yin gyaran otal ɗin saukar baki wato ‘Kongo Conference Hotel’, dake Zaria.
Hukumar EFCC ta kuma yi nuni da cewa bincikenta ya samu cewa sama da naira biliyan ɗaya, mutum biyun da ake zargi suka wawushe daga asusun ajiya daban-daban na jami’ar sannan suka karkata aƙalar su zuwa asusun ajiyar su.
Kotu Ta Yi Umarnin A Baiwa ‘Yar Sandan Da Ta Dauki Ciki Babu Aure Diyyar Miliyan N5m
A wani labarin na daban kuma, wata ta bayar da umurnin ga hukumar ƴan sanda ta biya wata jami’ar su kuɗin diyya.
Kotun masana’antu ta kasa da ke zama a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta yi watsi da dokar rundunar ‘yan sandan Najeriya NPF, da ta haramta wa matan da ba su da aure yin juna biyu, saboda sabawa sashe na 42 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi masa kwaskwarima) da tsari na 2 na Yarjejeniya Ta Afirka Kan Hakkokin Dan Adam da Jama’a wanda ya kawar da nuna bambanci dangane da jinsi.
A wani gagarumin hukunci da ya yanke a ranar Laraba, Mai shari’a Dashe Damulak ya kuma ce mai shigar da karar, Miss Omolola Olajide, na da damar kalubalantar kundin tsarin mulki na sashe na 127 na dokar ‘yan sanda da kuma doka ta 127.