Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta shiyyar Kano, a ranar Talata, ta ce ta kama wasu mutane 81 da ake zargi 68 daga cikinsu an same su da laifuka daban-daban a jihohin Kano, Jigawa, da Katsina, tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekara, Punch ta rawaito.
Kwamandan shiyyar Kano, Farouk Dogondaji ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta Kano Correspondents’ Chapel, da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa, ranar Talata.
KARANTA WANNAN: China Ta Kori Ministan Harkokin Wajen Kasar Kan Wasu Dalilai
Dogondaji ya ce shiyyar mai hedikwata a Kano ta kuma shafi jihohin Jigawa da Katsina.
A cewarsa, “Mun yi rokodin na kama mutane 81 bisa laifuka daban-daban na kudi a cikin watanni bakwai da suka gabata. Mun kuma tabbatar da hukuncin 68 daga cikin wadanda aka kama.”
Bugu da kari, ya bayyana cewa hukumar na ci gaba da rubuta wasu kararraki tare da yanke hukunci a shiyyar.
Kazalika, ya yi kira ga jama’a da kada su yi kasa a gwiwa wajen samar da bayanai masu amfani don baiwa Hukumar damar yaki da laifukan kudi a jihar.
Ya ce hukumar ta wuce gaban shari’a wajen kare laifuka, domin ta tsunduma cikin shirya tarurruka, lakcoci, bita da kuma karawa juna sani kan laifukan kudi, musamman a makarantun firamare da sakandare, inda ake koyar da yara ‘yan makaranta su tsaya tsayin daka da rayuwa ba tare da aikata laifukan kudi ba.
Ya kuma bayyana cewa hukumar EFCC a shiyyar ta kammala bincike kan wadanda ake zargi data kama yayin zaben 2023.
“Ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kotu. Lauyoyin mu na aiki da lauyoyin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ICPC domin gurfanar da su a gaban kotu,” ya kara da cewa.
Sai dai ya yabawa shugabannin kungiyar ta Kano Correspondents’ Chapel bisa hadin gwiwar da suka yi tare da yin alkawarin ci gaba da bunkasa dangantakar.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar masu aiko da rahotanni ta Kano, Alhaji Aminu Garko, ya yabawa kwamandan hukumar EFCC na shiyyar da tawagarsa bisa kyakkyawar tarba da suka yi musu.
Garko, ya roki hedkwatar EFCC da ta karkata akalar fitar da bayanai ga ‘yan jarida, ta yadda ‘yan Shiyyar za su samu damar baiwa ‘yan jaridun da ke aiki a shiyyar su bayanan da ake bukata domin yadawa cikin sauki.
A wani labarin kuma, Wata Kotu Ta Kori Karar ASUU, Ta Tabbatar Da CONUA, NAMDA
Shugaban Kotun Masana’antu ta kasa da ke Abuja, Mai Shari’a Benedict Kanyip, ya yi watsi da karar da kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta shigar na kalubalantar rajistar kungiyar (CONUA) da kungiyar (NAMDA).
Kotun ta tabbatar da CONUA da NAMDA a matsayin kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya ta yi wa rijista.