Hukumar EFCC, a ranar 3 ga watan Nuwamban 2022 ta gurfanar da Emmanuel Adeyi gaban babbar kotun Abuja da ke Gwagwalada gaban alkali I Mohammed bisa zarginsa da damfara, LIB ta ruwaito.
A wata takarda wacce EFCC ta saki, ta nuna yadda Emmanuel ya yi laifin a shekarar 2021 a Abuja inda ya dinga damfarar maza da sunan baamurkiyar karuwa mai suna Sally.
An bayyana yadda ya damfari maza $600 yayin da su ke tunanin karuwar su ka tura mawa. Don haka ake zarginsa da cuta ya hanyar sojan gona da sunan wata.
Ya amsa laifinsa inda aka yanke masa watanni uku a gidan yari tare da biya N30,000. Sannan Gwamnatin Tarayya ta amshe wayarsa kirar iPhone 12 Pro Max.
KU KARANTA: Bokanya ta afka gidan ‘yan damfarar yanar gizo, ta nemi su bata kasonta cikin kudin da su ka damfaro
Wata bokanya ta afka gidan wasu samari masu damfarar yanar gizo inda ta bukaci lallai sai sun raba kudaden da su ka damfaro da ita, LIB ta ruwaito.
A cewarta, tsafinta ya bayyana mata kudaden da su ka samu don haka ba za ta lamunce su ci kudin su kadai ba.
Bidiyon ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani da dama inda mutane su ka dinga mamakin karfin halinta.
An ji inda yake cewa tsafinta ya nuna mata kudaden da su ka samo a damfarar da su ka yi, don haka tazo da kanta ta amshi rabonta.