Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC a ranar Laraba ta sake bude kes din tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal bisa zarginsa da sama da fadi da naira miliyan 544 na kwangilar yankar ciyawa da aka ba shi.
EFFC ta sake bude kes din ne bayan da ta gurfanar da shaidarta na farko akan Lawal da wadansu mutum shida.
EFCC ta gabatar da Mohammed Babansule, Manaja da Bankin FCMB a matsayin shaida a shari’ar.
Manajan wadanda yake Manaja ne ga wanda ake kara na shida (Josmon Technologies Ltd) ya shaidawa kotu cewa takardar bude fom da wadansu takardu da aka gabatar ga bankin ya nuna cewa Apeh wanda ake kara na hudu shi ne mai asusun bankin. Kuma ya ce kamfanin ya bude asusun ne a 2015, kuma ya kulla alaka da shi ne a cikin watan Yunin 2018.