Eid-el-Fitr: FG ta amince da Alhamis a matsayin ƙarin hutun Sallah Ƙarama
Gwamnatin tarayya ta amince da ranar Alhamis a matsayin karin hutu domin murnar sallar Eid-El-Fitr ta bana.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Dr Aishetu Gogo Ndayako, babban sakatare na ma’aikatar harkokin cikin gida ya fitar ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yadda Babban Jojin Edo ya rantsar da Omobayo mai shekaru 38 a matsayin mataimakin gwamna
“Mai girma ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji Ojo, yayin da yake taya al’ummar musulmi murnar kammala wata guda na gudanar da ibada cikin nasara, ya nanata kudurin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR) na samar da zaman lafiya da wadata a Najeriya domin kowa ya samu ci gaba.” Sanarwar ta kara da cewa.
Tun da farko dai gwamnatin kasar ta sanar da ranar Talata da Laraba domin gudanar da bukukuwan Sallah Eid-El-Fitr amma ba a ga jinjirin wata ba a ranar Litinin, lamarin da ya sa aka tsawaita hutun.
DAILY POST ta tuna cewa Saudiyya da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar sun ayyana ranar Laraba 10 ga watan Afrilu a matsayin ranar karamar Sallah saboda ba a ga jinjirin wata ba.
A wani labarin kuma:Yadda Gobara ta shafi Ƴan Kasuwa 86 a Legas
Wani gini mai hawa uku mai shaguna 20 da shaguna guda uku ya kone kurmus a kasuwar Balogun da ke Legas a jiya, inda ya lalata kayayyakin miliyoyin naira.
Yan kasuwa tamanin da shida ne a bangaren kayan kwalliya da kayan da ake hada gashi ta lalata shagunansu. A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ba a samu asarar rai ba.