A wani hoto da Sanatan Kaduna ta Tsakiya ya fitar Malam Uba Sani ya nuna cewa, Tabbas Gwamna Nasir Ahmad El rufa’i na jihar Kaduna na cikin koshin lafiya.
Sanatan ya wallafa ya na mai nuna cewa, yau da safe su na kasar London tare da El’rufa’i, su na tattauna batutuwan da su ka shafi jihar Kaduna, da ci gaban ta.
Sanata Uba Sani ya wallafa cewa, “Ya ku al’ummar mu ta jihar Kaduna, Masoyan zuciyar mu, mun kasan ce a yau tare da Gwamna Nasir El-Rufai cikin yanayi mai kyau mara misaltu wa, domin tsara tunani, kamar yadda mu ka saba, mun kasan ce tare da sauran membobinmu a safiyar yau a kasar Landan, kan samar da hanyoyin ci gaba da dore war ci gaba a jihar Kaduna” inji Sanatan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cavani ba zai buga wasan Farko na Firimiya ba
Idan za’a iya tuna wa dai, tun da safiyar yau juma’a ce dai, kafofin sada zuminta na zamani su ka fara yada ra’de-ra’din cewa, an garzaya da Malam Nasiru Ahmad El rufa’i zuwa kasar London, sakamakon rashin lafiyar dake damunsa, Wanda wasu ke cewa a halin yanzu Gwamnan bai san a Ina ya ke ba.