Gwamnan Jahar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ragewa Shugaban Ma’aikatan sa muƙami Muhammad Sani Abdullahi ya zuwa Kwamishina mai kula da Hukumar tsare-tsare da Kasafin kuɗi.
Mr Abdullahi wanda akafi sani da Dattijo, ya taɓa zama kwamashina mai kula da Hukumar a wa’adin mulkin El-Rufa’i na farko.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Muyiwa Adekeye ya sanyawa hannu, El-Rufa’i ya kuma sanya sabbin muƙamai ga wasu kwamishinoni da wasu manyan jami’ai na Gwamnatin Jahar Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun fara Neman Dafaffen Abincin a Maimakon Kudin Fansa a Kaduna
Gwamnan yace jijjiga Manyan jami’an gwamnatin anyi shine domin taimakawa wajen sanya sabbin jini a ƙarshen wa’adin gwamnati, gami da kawo wasu sabbin canje-canje, domin baiwa Kwamishinonin samun gogewa a Gwamnati.
Acewar sanarwar, 8 daga cikin Kwamishinoni 14 an canja masu wuraren aiki.
Amma ba’ayi canji a Ma’aikatun Kuɗi da Shari’a, da Lafiya da Gidaje da bunƙasa birane, da kuma Ma’aikatar Harkokin Tsaron cikin gida da jindaɗin Al’umma.
Sabbin wuraren aikin da aka canjawa kwamishinoni sun ƙunshi:
Ma’aikatar Mahalli: Jaafaru Sani sai Ma’aikatar Ayyuka Thomas Gyang, da Ilmi: Halima Lawal da Noma: Ibrahim Hussaini, da Ƙananan Hukumomi: Shehu Usman Muhammad.
Sai Ma’aikatar tsare-tsare da Kasafin kuɗi Muhammad Sani Abdullahi, da Ma’aikatar Harkokin Kasuwanci, Kabir Mato, gami da Ma’aikatar Cigaban Wasanni Idris Nyam.
Biyo bayan aiwatar da dokar da zata bada damar kafa Hukumomi da zasu kula da garuruwan Kaduna da Kafanchan da Zaria, El-Rufa’i ya naɗa mutanen da zasu jagoranci Hukumar.