By Ishaq Dabai
Domin samun gudanar da shari’a ingantacciya da cin gashin kan shari’a, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba zai sanya hannu kan dokar, dokar Kula da Asusun Shari’a na Jihar Kano na shekarar 2021.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin Mako na kungiyar MAN ta Kasa na shekara ta 2021, wanda aka gudanar a dakin taro na Coronation dake Gidan Gwamnatin Kano a ranar Litinin.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Abba Anwar ya fitar, gwamna yana mai cewa “Na yi farin ciki cewa taron ya za a daidai lokacin da gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf don karba da sanya hannu a cikin dokar, muhimman kudurori uku da ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta mikawa majalisar dokokin jihar Kano.
Dokokin kuwa su ne Dokar Kula da gudanar da asusun Shari’a na Jihar Kano na 2021, da Alkalan Jihar Kano, da kuma Alkalan Kotun Shari’a da sauran Ma’aikatan Shari’a na 2021 da Dokar Kotun tafi da gidanka ta Kano na shekarar 2021. ”
Ya kuma tabbatar da cewa, da zarar majalisar dokokin jihar ta zartar da Kudirin, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar dasu da kuma tabbatar da cikakken zartar dasu.