- Tsohon dan wasan Liverpool, Graeme Souness ya caccaki ‘yan wasan Manchester United uku kan rawar da suka taka a kungiyar Red Devils
- Tsohon dan wasan ya ce ’yan wasan uku su ba komai ba ne, kuma ba su isa su buga wa Man United wasa na dogon lokaci ba
- Bana tunanin daya daga cikinsu ya isa ya zama dan wasan United na dogon lokaci kuma ya kai kulob din inda suke son zuwa a matsayin babbar gasar kwallon kafa ta duniya
Tsohon dan wasan Liverpool, Graeme Souness ya caccaki ‘yan wasan Manchester United uku Jadon Sancho, Antony da Alejandro Garnacho, kan rawar da suka taka a kungiyar Red Devils kawo yanzu a kakar wasa ta bana.
Souness ya ce Sancho, Antony da Garnacho ’yan wasa ne da ba komai ba, ya kara da cewa ba su isa su buga wa Man United wasa na dogon lokaci ba.
KARANTA WANNAN: Musaya: An Tabbatar da Dawowar dan Wasa Sanchez Zuwa Tsohon Kulob din Sa
Dan wasan ya bayyana hakanne gabanin wasan Premier da Man United za ta yi da Nottingham Forest ranar Asabar a Old Trafford.
“A kan fuka-fukai, kuna kallon Jadon Sancho, Antony da Alejandro Garnacho,” Souness ya rubuta a cikin shafin Daily Mail.
“Bana tunanin daya daga cikinsu ya isa ya zama dan wasan United na dogon lokaci kuma ya dauki kulob din ya kai shi inda suke son zuwa a matsayin babbar gasar kwallon kafa ta duniya su ba komai ba ne.”
A wani labarin kuma, Dan Wasan Tsakiya Na Portugal Ya Bar Porto Ya Koma Saudiyya Zai Hadu da Ronaldo
Dan wasan tsakiya Otavio ya bar Porto zuwa kulob din Al-Nassr na Saudiyya a kan yarjejeniyar kudi Yuro miliyan 60 wanda yayi dai dai da (dala miliyan 65.1), in ji kulob din Portugal a ranar Talata.
Otavio wanda haifaffen dan kasar Brazil ne ya koma Porto ne a shekara ta 2014 daga Internacional kuma ya fara buga wa kasarsa ta Portugal wasa a shekarar 2021.
Zai haɗu da abokin wasan Portugal Cristiano Ronaldo a Al-Nassr.
“Yana da wuya a bar kulob din bayan shekaru tara a nan,” dan wasan mai shekaru 28 ya shaida a gidan yanar gizon Porto.
Otavio ya zama sabon dan wasan da ya koma Saudi Pro League bayan manyan mutane kamar su Ronaldo, Karim Benzema, N’Golo Kante, Ruben Neves da Roberto Firmino da sauransu.