- Tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ya jinjinawa Arteta kan namijin kokarinsa na horas da yan wasan kungiyar
- Jawabin Wenger na zuwa ne bayan nasarar Arsenal a wasan ta da kungiyar Norwich da aka tashi da ci 1-0
- Arsenal dai ta sha kaye a wasannin farko da ta buga tun da aka fara kakar wasannin bana
Kungiyar, dake a kasar Landan ta Arewa, ta ajiye tarihi na buga wasanni uku ba tare da maki ba, kuma ba tare da saka kwallo ko daya a raga ba, gami da fuskantar zura kwallaye tara a ragar su.
Haka zalika, wannan nasara da aka samu akan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ya sanya ta koma na sha shida a teburin masu cin kofin.
Wenger ya shaida wa majiyar jaridar Dimokuradiyya cewa, “ina son fadin abinda nake tunani, na yi imani akan wannan lamarin cewa ina cikin sahun farko na masoyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, domin idan nayi magana akan Arsenal, to abune da yake mai wahala , kuma a yanzu ba lokaci bane da ya kamata in yi magana la’akari da lokaci.
“Amma zan iya cewa na samu tawaga da ta kware, bana jin bakin ciki, domin naji cewa sun rasa wasanni guda biyu daga cikin uku da suka buga”.