By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya a ranar Talata ta dakatar da jirgi mai lamba VM1609 na kamfanin MaxAir, domin gudanar da aikin duba lafiyar jirgin bayan fasinjoji sun hau kuma tuni ya hau layi domin tashinsa. An tattaro cewa fasinjojin jirgin da ya tashi daga filin jirgin saman Abuja zuwa Legas, sun yi tur da tsaikon da hukumar ta NCAA ta haifar.
Rahotanni sun ce wasu matafiya sun koka da yadda suka makale a cikin jirgin, saboda sun yi zargin cewa an dakatar da jirgin ne saboda wasu matsaloli.
Wani fasinja wanda ya bayyana sunansa da Raymond, ya ce jirgin da ya tashi da karfe 11:30 na safe ya dan yi nisa ne a wurin da ake shirya titinsa don tashi kafin daga bisani a dakatar da tashin sa.
Da aka tuntubi Manajan tashar MaxAir a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, Kehinde Ogunyale, don bayyana hakikanin abin da ya faru, ya ce dole jirgin ya bi ka’idojin hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama-NCAA.
“Wannan jinkiri ne kawai a cikin jirgin, babu wani abu kamar fasinjojin da suka makale don Allah, kuma saboda an gaya mana cewa NCAA na son yin bincike. Haka ne,” ya shaida wa wakilinmu.
Ogunyale ya kara da cewa, “Don haka jinkirin ya zo ne saboda muna jiran hukumar NCAA ta gudanar da binciken. Babu wani abu kamar fasinjoji da suka makale a cikin jirgin namu.
“Jirgin na shirin tashi kuma sun ce suna son yin bincike a kan jirgin. Don haka lokacin da aka kashe yana da nasaba da jiran jami’an NCAA su yi binciken.
“Bayan an duba, jirgin na nufin tashi ne kuma kamar yadda nake magana da ku yanzu na samu labarin cewa yanzu jirgin yana kan layi don tashi.”
An tattaro cewa daga karshe jirgin ya tashi da misalin karfe biyu na rana bayan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kammala aikin duba lafiyar jirgin.
Ko da yake mai magana da yawun hukumar ta NCAA, Sam Adurogboye, ya bayyana cewa har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin MaxAir a Abuja lokacin da aka tuntube shi ba, ya bayyana cewa ya dace a duba jirgin sama, musamman a duk lokacin da matukin jirgin ya nuna damuwa.
“Matukin jirgin zai iya lura da wata matsala kuma zai iya kiran hukumar NCAA don duba jirgin. Don haka ya dace a gudanar da irin wannan binciken kafin a share jirgin domin tashinsa,” inji shi.