Gwamnatin tarayya ta fara biyan wasu malaman jami’o’in CONUA da suka balle daga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) albashin watanni 8.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da mambobin majalisar zartaswar kungiyar ASUU ta kasa suka kammala shirye-shiryen gudanar da taron gaggawa da nufin magance matsalar biyansu “rabin albashi”.
Wani mamba na kungiyar CONUA kuma malami a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile Ife, wanda ya bayyana wa majiyar DIMOKURADIYYA da bai yarda a bayyana sunansa ba a daren Lahadi, ya ce tuni shugabannin kungiyar suka samu ra’ayi daga Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige.
KU KARANTA KUMA Yadda Dan Shekaru 32 Ya Yi Wuf Da Mata Uku Lokaçi Guda
Jami’in ya kuma ce ministan ya tabbatar wa mambobin sabuwar kungiyar cewa za su fara karbar sanarwar tun daga ranar Litinin, ya kuma yi alkawarin cewa za a warware matsalar “rabin albashi” da aka ba su.
“Ba mu kasance cikin yajin aiki na karshe ba. A baya mun rubutawa ma’aikatar kwadago da samar da ayyuka ta tarayya. Don haka, ministan ya duba wasikar tamu, kuma ya ba da umarnin hakan,” in ji jami’in.
Kokarin jin ta bakin Ko’odinetan CONUA na kasa, Niyi Sunmonu, ya ci tura saboda kiran wayarsa ya ki shiga. Har yanzu bai mayar da martani ga sakon da aka aike masa ba zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Da aka tuntubi mai magana da yawun Ministan, Olajide Oshundun, ya tabbatar da cewa za a biya ‘yan kungiyar ta CONUA albashi matukar ba sa cikin yajin aikin da ya kwashe watanni takwas ana yi.
Ya ci gaba da cewa ba za a biya wadanda suka shiga yajin aikin ba tunda har yanzu manufar Babu aiki babu biya’ ta nan.
“Abin da zan iya fada muku da nake da matsayin mai magana da yawun shi ne, manufar ‘Babu aiki-ba bu biya’ ya rage. Hakan bai canza ba domin lamari ne da ya shafi tsarin mulki. Haka kuma an yarda da Yarjejeniya ta ILO cewa idan mutane suka tafi yajin aiki ba za a iya biyan su ba.
“Don haka, idan CONUA ba ta shiga yajin aikin ba, suna da hakkin samun kudadensu. Amma idan sun shiga yajin aikin, su ma ba za a biya su ba. Idan ba su yi yajin aiki ba, bisa doka da ka’ida, suna da hakkin a biya su albashi. Ina kallon hakan ta hanyar doka, ”in ji shi.
A Wani Labarin Kuma Buhari Zai Bunkasa Noma Domin Wadatar Abinci Har A Fitar Da shi Kasashen Waje
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen bunkasa noma domin bunkasa noma na da darajarsa, domin tabbatar da wadatar abinci a kasar da kuma fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen waje.
Shugaban ya kuma ce a karshen gwamnatin sa zai bar Najeriya cikin hadin kai da wadata da kwanciyar hankali fiye da yadda ya gamu da ita.