Akwai dimbin jami’an tsaro a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa a Filato domin gudanar da zaben cike gurbin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bassa/Jos ta Arewa.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da ya ziyarci wasu yankunan ya ruwaito cewa, an jibge tawagar jami’an tsaro ta a rumfunan zabe,da sauran wurare masu muhimmanci.
Shugaban ‘yan sandan jihar, Batholomew Onyeka, ya ce ya tura ‘yan sanda da dama domin ganin an gudanar da zaben cikin lumana.
Ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta hana zirga-zirgar ababen hawa tsakanin karfe 12 na dare zuwa karfe 6 na yamma, ban da wadanda ke da muhimman ayyuka.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Ogaba, ya shaida wa NAN cewa tura jami’an ‘yan sandan ba wai don tsoratar da masu kada kuri’a ba ne, sai dai don tabbatar da an gudanar da aikin ba tare da wata matsala ba.
“Abin da muke so shi ne tsarin zaman lafiya kuma muna kira ga mazauna yankin da su gudanar da rayuwarsu cikin lumana a lokacin zabe da kuma bayan zabe”.
Ogaba ya bukaci jam’iyyun siyasa da su ja kunnen magoya bayansu da su daina haifar da rikici a lokacin zabe