By Abbas Yakubu Yaura
Firaministan farar hula na kasar Sudan Abdalla Hamdok ya yi murabus jiya Lahadi, sama da watanni biyu bayan juyin mulkin da ya biyo bayan wani mumunar murkushe masu gudanar da zanga-zangar nuna adawa, inda a yanzu sojoji ke da karfin iko.
Kasar Sudan dai na fama da matsananciyar tafiya ta neman mulkin farar hula tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekara ta 2019, amma ta fada cikin rudani lokacin da shugaban soji Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kaddamar da juyin mulkin a ranar 25 ga watan Oktoba tare da tsare Hamdok.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an mayar da Hamdok kan mukaminsa ne a ranar 21 ga watan Nuwamba bisa yarjejeniyar da ta yi alkawarin zabuka a tsakiyar shekarar 2023, sai dai a baya-bayan nan kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa ya yi kwanaki ba ya nan a ofishinsa, inda ake ta yada jita-jita game da yiwuwar yin murabus dinsa.
“Na yi iya kokarina na hana kasar karkata zuwa ga bala’i,” in ji Hamdok a yammacin Lahadi, yayin da yake jawabi ga al’ummar kasar a gidan talabijin na kasar.
Sudan “tana tsallake wani yanayi mai hatsarin gaske wanda ke barazana ga rayuwarta baki daya,” in ji shi.
Hamdok dai ya kasance fuskar farar hula na sauyin yanayi a kasar, yayin da Burhan ya kasance shugaban kasar na gaskiya bayan hambarar da Al-Bashir.
Hamdok ya ba da misali da “raguwa na ‘yan siyasa da rikice-rikice tsakanin (sojoji da na farar hula) na mika mulki” ya kuma ce “duk da abin da aka yi don cimma matsaya bai faru ba”.
An ga wasu matasa a kan babura suna jigilar masu gudanar da zanga-zangar da suka samu raunuka zuwa asibitoci yayin da jami’an tsaro suka hana motocin daukar marasa lafiya zuwa wurinsu.
Kungiyar sa ido ta yanar gizo ta NetBlocks ta ce an katse ayyukan sadarwar intanet ta wayar hannu tun da sanyin safiya gabanin zanga-zangar, farkon shekara kafin da yamma aka mayar dasu.
Masu fafutuka suna amfani da kafar sadarwar intanet don shirya zanga-zanga da watsa faifan gangamin kai tsaye.
Zanga-zangar da aka yi tun bayan da sojojin suka karbe iko jami’an tsaro na ci gaba da wargaza masu zanga-zangar da suka yi ta harba hayaki mai sa hawaye, da kuma zargin ‘yan sanda na amfani da sanduna.
A ranar Juma’a wani mai ba da shawara a hukumance ya yi gargadin cewa zanga-zangar “ɓatacciya ce na kuzari da lokaci” wanda ba zai haifar da “kowace mafita ta siyasa ba”.
Masu fafutukar sun kuma yi Allah wadai da hare-haren ta’addanci a lokacin zanga-zangar ranar 19 ga watan Disamba, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mata da ‘yan mata 13 ne aka yi musu fyade ko kuma fyaden gayya.
Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi Allah wadai da amfani da cin zarafin mata “a matsayin makami don korar mata daga zanga-zangar da kuma rufe muryoyinsu”.
A ranar Asabar, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi gargadin cewa, Washington ta “shirya don mayar da martani ga wadanda ke neman dakile muradun al’ummar Sudan na kafa gwamnatin farar hula, da mulkin dimokuradiyya, da kuma wadanda za su tsaya a kan hanyar da za a bi wajen tabbatar da gaskiya da adalci, lafiya”.
Sama da mutane miliyan 14, daya daga cikin uku na Sudan, za su bukaci agajin jin kai a cikin shekara mai zuwa, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD – matakin mafi girma na tsawon shekaru goma.AFP