Fitaccen Mawaƙi Mr P, ya hana duk wanda bai da Katin Zaɓe daga ziyartar sa
Gabanin Babban Zaɓen Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023, Fitaccen Mawaƙi a Najeriya Peter Okoye da akafi sani da Mr P, ya bayyana cewa zai daina karɓar duk wani wanda bai da Katin Zaɓe daga Ziyartar sa.
Mr P, daya daga cikin tagwaye na P Square ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a shafin sa na Twitter a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnoni sun miƙa sunayen Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa 5 ga Buhari, an cire Ahmed Lawan daga ciki
Mawaƙin yace baiwa Jami’an tsaron sa umarni da kada su bar kowa yazo wurin sa, ba tare da katin zaɓe na Din-Din-Din.
“Yanzu na baiwa Jami’an tsaro na umarni cewa kada wanda aka bari ya ziyarce ni gidana ko ofishina ba tare da ya nuna PVC na shi ba.”
“Har da Shuwagabanci na da tawaga ta cewa babu Kati! Babu ziyara! Dole mu kori Shuwagabannin mu ruɓaɓɓu. Ya rubuta a Twitter.
Za’a fara Zaɓen Shugaban Ƙasa a ranar 25 ga watan Fabrairu na Shekarar 2023. Tun 2019, kimanin mutane miliyan 20 ƴan Najeriya suka zamanto suna da Shekaru 18, kuma zasu iya zaɓe.