By Abbas Yakubu Yaura
Ministan wasanni na Najeriya, Sunday Dare ya ba da umarnin rufe filin wasa na Moshood Abiola, babban filin wasa na Abuja.
Dare ya yanke shawarar ne bayan da kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya koka game da rashin kyawun yanayin wasan bayan horo na ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fitaccen Mawaƙi Mr P, ya hana duk wanda bai da Katin Zaɓe daga ziyartar sa
Su ma Super Eagles din ba su yi atisaye a filin wasa ba a ranar Litinin din da ta gabata don ba wa ‘yan wasa damar sanya shi cikin tsari mai kyau kafin wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2023 da za a yi a ranar Alhamis da Leone Stars ta Saliyo.
Sun yi atisayen ne a ranar Litinin a filin atisaye na filin wasan.
“Za a iya amfani da filin wasan ne kawai don wasanni da suka shafi kungiyoyin kasa,” wani jami’in ma’aikatar wasanni Mohammed Manga ya shaida wa NAN.
“Dole ne mu kiyaye babban filin wasan cikin kyakkyawan tsari don amfani da wasannin kasa da kasa da suka shafi kungiyoyin kasa,” in ji shi.
Da wannan ci gaban, kungiyar kwallon kafa ta Nigeria Professional Football League, Kano Pillars za ta nemi sabon filin wasa domin buga wasanninta na gida.
Hukumar kula da gasar League ta kore su Sai Masu Gida a Abuja sakamakon rikicin da suka yi a gidansu da Katsina United.
Comments 1