Gwamnatin jihar Ribas ta shirya hada kai a Gwamnatin tarayya, domin aiki tare wajen habbaka tattalin arzikin jihar.
Nasarar hakan zata tabbata ne bisa jagorancin Zaɓaɓɓen gwamnan jihar mai jiran Gado Siminialayi Fubara.
Kwamishinar yada labarai na jihar Ribas Chris Finebone ne ya bayyana hakan, Yayin ganawa Da manema labarai s birnin Fatakwal Alhamis din nan.
KU KARANTA: Tsohon Minista da Wani Sun Shiga Ha’ula’i, Kotu Ta Amince a Cafko Su
Ya kuma zayyanar da wasu daga cikin shirye shiryen da kwamitin su ke yi domin karbar sabuwar gwamnati, wadda ake shirin rantsar da ita nan da wasu kwanaki kadan masu zuwa.
Finebone dai shine sakataren yada labarai na kwamitin kaddamar da sabuwar gwamnati, wanda yanzu haka shiri kuma yayi nisa wajen ganin an mika tare da karbar mulkin cikin ruwan sanyi.
Ya kara da cewa Gwamna Fubara mai jiran rantsuwa ya shirya samar da hanyoyi masu tarin yawa, wadanda zasu taimaka wajen ci gaban jihar Ribas.
A wani labarin kuma: Dawa Tai Nama: NDLEA Ta Cafke Mutane 34 Da Ake Zargi da Shan Miyagun Kwayoyi
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kame wasu mutane 34 a Abuja.
Ya zama wajibi a gudanar da aikin simamen saboda bukatar yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi
NDLEA ta ce za a ci gaba da kai farmakin har sai hukumar ta kawar da miyagun kwayoyi domin rage yawan aikata laifuka.