Jami’an tsaron farin kaya na DSS a jihar Kano sun cafke matashin nan Baffa Hotoro.
An cafke matashin ne bayan da ake zargin sa sakin baki wajen yin kalaman da basu kamata ba ga shugaban halitta SAW.
KU KARANTA: Dawa Tai Nama: NDLEA Ta Cafke Mutane 34 Da Ake Zargi da Shan Miyagun Kwayoyi
A watan azumin da ya gabata ne Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa jami’an tsaro tuni sun samu nasarar damƙe matashin.
To sai dai da mamakin daga bisani, bayan kalaman gwamnan sai Baffan ya fito a bidiyo ya musanta cewa an kama shi.
Amma a Alhamis ɗin nan hukumar DSS a Kano ta tabbatar wa da gidan Radio Freedom, cewa suna tsare da matashin wato Baffa Hotoro.suna ci gaba da gudanar da bincike akansa.
Irin wadannan kalamai da basu kamata daga wasu daga cikin malamai, na ci gaba da yawaita a tsakanin malaman addinin Musulunci, lamarin dake bukatar mahukunta su kara zage damtse.
A wani labarin kuma: Fubara Da FG Zasu Hada Kai Domin Bunƙasa Jihar Ribas
Gwamnatin jihar Ribas ta shirya hada kai a Gwamnatin tarayya, domin aiki tare wajen habbaka tattalin arzikin jihar.
Nasarar hakan zata tabbata ne bisa jagorancin Zaɓaɓɓen gwamnan jihar mai jiran Gado Siminialayi Fubara.
Kwamishinan yada labarai na jihar Ribas Chris Finebone ne ya bayyana hakan, Yayin ganawa Da manema labarai s birnin Fatakwal Alhamis din nan.