Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da wasu mutane masu mutunci a kasa da duniya baki daya, kan yadda za a kawo karshen kalubalen da bangaren lafiya a jihar ke fuskanta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa manufar yarjejeniyar itace tabbatar da ingantuwar tsarin kiwon lafiya a Kano, do Amfanar al’ummar ta.
Taron dai ya gudana ne a dakin taro na Afrika House dake gidan Gwamnati, wanda kuma ya samu halartar mukarraban gwamnati da sauran manyan baki.
Daga cikin bangarorin da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya sun haɗar da gidauniyar Alhaji Aliko Dangote, da Bill da Milinda Gates, da Asusun tallafawa ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da kuma hadin gwiwar gwamnatin tarayya.
KARANTA ANAN: ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Tsohon Soja Mai Yi Wa ‘Yan Ta’adda Safarar Makamai
Dr Faisal Shu’aib shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa, shima ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin tarayya.
Yayin da mai martaba sarkin Kano shima ya wakilci hukunar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, a matsayin wanda ya sanya ido kan tabbatuwar shirin.
Ya kuma tabbatar da cewa wannan tsarin zai taimakawa bangaren lafiya na jihar wajen ingantuwarsa, kuma babba nasara ce kasancewar jihar Kano cikin wannan yarjejeniyar.
Daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa sun haɗar da:
Tabbatar da ingantuwar tsarin alluran riga-kafi, ta hanyar samar da karin wadatattun kudade, da kuma tabbatar da an inganta tsarin bayar da lafiya a yankunan musamman dake cikin kauyuka wajen ganin lafiyar su ta inganta.
A yayin taron sun kuma yabawa gwamnan kan yadda yake aiki tukuru bangaren lafiya na jihar, inda suka ce hakika hakan zai taimaka wajen ingantuwar bangaren lafiya na jihar na baki daya.
Da yake nasa jawabin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da ci gaba da bayar da dukkanin gudunmawar data kamata, wajen ganin al’ummar Kano sun sami ingantacciyar lafiya.
Ya kuma tabbatar da yin duk mai yiwuwa wajen ganin Yarjejeniyarsu ta samu Tagomashi da kuma tabbatuwa.
A wani labarin kuma: Bayan Shafe Kwanaki 174, Ƴan Boko Haram Sun Sako Ma’aikacin Agaji
Mohammed Alkali Imam, ma’aikacin kwamitin ceto na kasa da kasa (IRC) wanda kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da shi a ranar 10 ga Maris, 2022, masu garkuwa da mutane sun sako shi.
An dai yi garkuwa da Imam ne a yankin Monguno da ke jihar Borno a lokacin da wasu mahara suka kai masa hari inda suka kai shi da karfi.