Ganduje ya kafa kwamiti yayin da rikicin tsige gwamnatin Ondo yake ƙara ta’azzara
A ranar Alhamis din nan ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, Alhaji Abdullahi Ganduje a Abuja ya kafa kwamitin mutane tara domin shiga tsakani a rikicin tsige gwamnatin jihar Ondo.
Mista Edwin Olofu, babban sakataren yada labarai na Ganduje ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Juyin mulki: Afirka na bukatar sake dawo da martabar mulkin dimokuradiyya – Jonathan
Ya ce kwamitin karkashin jagorancin Aminu Masari, tsohon gwamnan jihar Katsina, zai kuma nemi a sasanta duk bangarorin da abin ya shafa.
“Gaskiya babbar sakatariyar jam’iyyar ta kasa ta damu da irin halin da ake ciki a siyasance a jihar Ondo, wanda idan ba a gaggauta kawar da shi ba, zai iya haifar da rashin jituwa a tsakanin mabiya jam’iyyar.
“Saboda haka, domin a kawar da rashin fahimtar juna, kuma bayan lura da lamarin, sakatariyar kasa ta yanke shawarar kutsa kai.
“Da nufin samar da ingantacciyar fahimtar da za ta iya kaiwa ga cimma matsaya ta gaskiya,” in ji Ganduje.
Ya kuma tabbatar wa ‘ya’yan jam’iyyar cewa kwamitin zai yi mu’amala tare da tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar bisa mutunta juna, da nufin samar da mafita mai dorewa a kan rikicin.
Ya kuma bukaci dukkanin bangarorin da su kwantar da hankulansu tare da baiwa kwamitin da Masari ya jagoranta hadin kai da goyon baya.
A wani labarin kuma:WHO ta saki dala miliyan 16 don magance cutar kwalara
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da dala miliyan 16 daga asusun ba da agajin gaggawa na WHO don magance cutar kwalara.
Darakta-Janar na WHO, Dr Tedros Ghebreyesus ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ta yanar gizo.