WHO ta saki dala miliyan 16 don magance cutar kwalara
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da dala miliyan 16 daga asusun ba da agajin gaggawa na WHO don magance cutar kwalara.
Darakta-Janar na WHO, Dr Tedros Ghebreyesus ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ta yanar gizo.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zaben Gwamnan Kano: NNPP Ta Caccaki Ganduje Kan Kalaman Sa Ga Kwankwaso
Ghebreyesus ya ce, Hukumar tana samar da muhimman kayayyaki, tana daidaita martanin kan kasa tare da abokan hulda, tallafawa kasashe don ganowa, rigakafin cutar kwalara, da kuma sanar da mutane yadda za su kare kansu.
“Don tallafa wa wannan aikin, mun nemi dala miliyan 160, kuma mun saki sama da dala miliyan 16 daga Asusun Tallafawa na gaggawa na WHO.
“Amma don ainihin magance cutar kwalara ta ta’allaka ne wajen tabbatar da cewa kowa ya samu tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli, wanda hakkin bil’adama ne da duniya ta amince da shi,” in ji shi.
A cewarsa, a cikin makon da ya gabata, WHO ta buga sabbin bayanai da ke nuna cewa adadin wadanda aka samu a shekarar 2022 ya ninka na shekarar 2021.
Ya ce bayanan farko na shekarar 2023 da aka nuna wa na iya zama mafi muni.
Ya zuwa yanzu, kasashe 28 ne suka bayar da rahoton bullar cutar a shekarar 2023 idan aka kwatanta da 16 a daidai wannan lokacin a shekarar 2022.
“Kasashen da suka fi fama da barkewar cutar a yanzu su ne Habasha, Haiti, Iraki da Sudan.
Ghebreyesus ya ce “An samu gagarumin ci gaba a kasashen dake kudancin Afirka, ciki har da Malawi, da Mozambique da Zimbabwe, amma wadannan kasashe na ci gaba da fuskantar hadari yayin da damina ke gabatowa.”
A cewarsa, kasashen da lamarin ya fi shafa talakawa ne, ba tare da samun tsaftataccen ruwan sha ko bandaki ba.
Ya ce, suna fuskantar karancin allurar rigakafin cutar kwalara da sauran kayayyaki, da ma’aikatan kiwon lafiya masu yawa, wadanda ke fama da barkewar cututtuka da dama da sauran matsalolin kiwon lafiya na gaggawa.
A wani labarin kuma:Juyin mulki: Afirka na bukatar sake dawo da martabar mulkin dimokuradiyya – Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce juyin mulkin da ake fama da shi a nahiyar Afirka a halin yanzu ya nuna cewa akwai bukatar a “juya wa dimokuradiyya” da kuma dora ta a kan turbar da ta dace.
Jonathan ya bayyana haka ne a yayin taron tattaunawa na dimokuradiyya 2023 da gidauniyar Goodluck Jonathan (GJF) ta shirya mai taken: “Breaking New Grounds In The Democracy Development Nexus in Africa” a Yenagoa.