- Dan wasan gaba na Sion, Mario Balotelli, ya yi hasashen cewa Inter Milan ce zata yi nasara a wasan da za su yi Manchester City.
- “Inter tana da ‘yan wasa da yawa da za su iya yin bambanci da Man City.”
- Balotelli yace kwarewa ta nuna masa cewa yana da kyau a isa wasan karshe a matsayin marasa karfi tsakanin kungiyoyin biyu.
Dan wasan gaba na Sion, Mario Balotelli, ya yi hasashen cewa Inter Milan na daga cikin wadanda zasu yi nasara a wasan da za su iya bata wa Manchester City rai a lokacin da kungiyoyin biyu zasu kara a wasan karshe na gasar zakarun Turai na ranar 10 ga watan Yuni a Turkiyya,kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Balotelli, wanda tsohon dan wasan Manchester City da Inter Milan ne, shi ma ya ware wasu manyan ‘yan wasa irin su Lautaro Martinez, Romelu Lukaku da Edin Dzeko domin yaba musu.
KARANTA WANNAN: NBC Ta Baiwa Wata Kwalejin Fasaha Lasisin Gudanar Da Aikin Gidan Rediyo
Dan wasan mai shekaru 32 ya lashe kofuna tare da kungiyoyin biyu a zamansa a filin wasa na Etihad da kuma San Siro.
“Inter tana da ‘yan wasa da yawa da za su iya yin bambanci [da Man City],” Ballotelli ya shaida wa La Gazzetta dello Sport.
“Tun daga abokina Dzeko, amma kuma ban manta da Lukaku da Lautaro ba, kwallonsa ta biyu a kan Fiorentina ta yi kyau.
“Kwarewa ta nuna min cewa yana da kyau a isa wasan karshe a matsayin marasa karfi. Kuma, yayin da kungiyar Guardiola ke taka rawar gani a wasan kwallon kafa, kungiyar Inzaghi ma tana da kwarewa,” in ji shi.
A wani labarin kuma, ‘Shanu Da Tumaki Na Sun Fi ‘yan Najeriya Saukin Sarrafawa’ – Buhari
Shugaban Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya ce zai bukaci a rage yawan shanu da tumaki da ke gonarsa.
Buhari yace saboda ba zan samu isassun kudin da zan sayo musu abinci ba bayan na sauka daga karagar mulki.
Buhari ya kara da cewa shanu da Tumaki na sun fi ‘yan Najeriya saukin sarrafawa,