- Hukumar kula da kafafen Yada Labarai ta Kasa NBC ta bai wa kwakejin Fasaha ta Ibadan lasisin bude gidan rediyo.
- Lasisin na ɗan wani lokaci ne inda za’a jira cikar sauran bayanan biyan kuɗin da ake buƙata.
- Kwalejin Fasahar za ta gabatar da aikace-aikacen gudanar da gidan rediyon da aka gabatar ga
hukumar.
Hukumar kula da kafafen Yada Labarai ta Kasa NBC ta bai wa kwakejin Fasaha ta Ibadan lasisin gudanar da aikin gidan rediyo.
Kwalejin ta bayyana hakan ne ta wata sanarwa mai dauke da rattaba hannun rijistarar ta, Misis Modupe Theresa Fawale.
KARANTA WANNAN: DA Dumi-Dumi: Wasu Fusatattun Matasa Sun Rufe Wani Gidan Rediyo a Najeriya
DAILY POST ta tattaro cewa an baiwa cibiyar lasisin gudanar da aikin gidan rediyon Kwalejin Fasaha Ibadan FM.
An isar da haƙƙin gudanar da gidan rediyon zuwa cibiyar ta hanyar wasiƙar da ta fito daga ofishin NBC mai lamba NBC/SEC/LIC/19/VOL.iv mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Mayu 2023.
Wasikar wacce aka aikewa shugaban cibiyar, Farfesa Kazeem Adekunle Adebiyi, ta samu sa hannun sakataren hukumar Igomu Onoja a madadin babban daraktan hukumar NBC.
Fawale ya ce, “An mika wa hukumar ‘yancin gudanar da gidan rediyon FM ne ta wata wasika daga Hukumar NBC mai lamba NBC/SEC/LIC/19/VOL.iv mai kwanan wata 22 ga watan Mayu, 2023 zuwa ga Shugaban Cibiyar Farfesa Kazeem. Adekunle Adebiyi.
“Wasikar mai dauke da sa hannun sakataren hukumar Igomu Onoja a madadin Daraktan Janar ya lura cewa lasisin na ɗan lokaci ne inda za’a jira cikar sauran bayanan biyan kuɗin da ake buƙata.
“Cibiyar za ta gabatar da aikace-aikacen gudanar da gidan rediyon da aka gabatar ga
hukumar.”
A wani labarin kuma, Huce Ta Kaici: Obi Bai Shirya Zanga-Zanga Ba, Ba Zai Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu Ba – Hadimi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce zai zama da ‘matukar ban mamaki’ ya halarci bikin rantsar Tinubu.
Obi ya musanta shirin gudanar da zanga-zanga gabanin rantsar da zababben shugaban kasa mai jiran gado a yau 29 ga watan Mayu.
Wannan martani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar Anambra da kungiyarsa ta Obident za su gudanar da zanga-zanga a dandalin Eagle Square.