Gawamnati za ta gurfanar da masu Ababen Hawa Sama da 200 A Gaban Kotu kan Laifuka daban-daban
Hukumar kula da babban birnin Tarayyayya Abuja ta ce masu motoci 149 da aka kama da babura 100 a babban birnin tarayya Abuja za su gurfana a gaban kotun tafi da gidanka bisa laifuka daban-daban.
Dr Abdulateef Bello Daraktan Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta FCTA wanda aka fi sani da VIO ya bayyana haka a Abuja ranar Juma’a bayan ya duba motocin da aka kama.
Bello wanda ya ziyarci wasu daga cikin Ofisoshin VIO inda ake ajiye Ababen hawan da aka kama, ya ce masu za su biya maƙudan kuɗaɗe a matsayin tara.
Ya bayyana cewa laifukan sun haɗa da ajiye Motoci a wuraren da ba a ba su izini ba, da keta dokokin zirga-zirga, da tasi marasa rajista da fenti da kuma ajiye Motoci ba bisa ka’ida ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Zamfara Ta Gayyaci Shugabannin Tsaro Kan Sace Daliban Jami’ar Tarayya
“A koyaushe ina ba da shawarar cewa yana da kyau mutum ya kasance yana bin doka da ƙa’idodin tuƙi domin samun salama”.
“Mun nemi masu ababen hawa da su yi rajista, kuma su yi aiki a cikin ƙayyadaddun hanyoyin mota da wuraren ajiya na motoci, tare da ƙoƙarin kiyaye dukkanin dokokin hanyoyin”.
“Mun kuma gaya wa masu babur da su yi aiki a cikin iyakokin da aka riga aka amince da su”.
“Bai kamata su shigo cikin birni ba, Ya kamata su yi jigilar mutanen da ke shiga cikin Unguwanni da ke bayan gari,” inji shi.
Ya ce an sake duba ka’idojin zirga-zirga inda ya ƙara da cewa za a sake duba yiwuwar ƙara kuɗaɗen tara.
Ya ce masu laifin za su biya maƙudan kuɗaɗe idan sun fuskanci kotu “amma na tabbata hakan zai zama mafita”
Daraktan ya ce, yana aiki tare da sakatariyar harkokin sufuri na hukumar babban birnin tarayya don duba manufofin zirga-zirgar ababen hawa da ake da su a kan tafiyar da ababen hawa.
Hakan a cewarsa zai tabbatar da ingantaccen tsarin kula da ababen hawa a Abuja.