Wani yaro dan shekara 17 ya kashe kansa a garin Makurdi
Wani matashi dan shekara 17 da ake zargin Ɗalibin Babbar Makarantar Sakandaren Gwamnati ne ta Gboko a ƙaramar Hukumar Gboko a Jihar Benue Terhemba Tyochivir ya kashe kansa.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani kan lamarin, amma an tattaro cewa marigayin ya rataye kansa da yammacin ranar Alhamis a unguwar Akpehe da ke garin Makurdi.
A cewar majiyarmu “babu wanda zai iya bayyana dalilin da ya sa ya kashe kan sa, amma da makwabta suka tsinto gawarsa daga wurin sai suka garzaya da ita Asibitin Gwamnati da ke unguwar High Level a garin inda aka tabbatar da mutuwarsa.
A dai dai lokacin da aka gano gawarsa a wurin da lamarin ya faru an kai rahoto ga ‘yan sanda da ke ‘E Dibision’ a Makurdi, inda daga nan aka garzaya da shi asibiti.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Zamfara Ta Gayyaci Shugabannin Tsaro Kan Sace Daliban Jami’ar Tarayya
Kafin rasuwarsa an ce shi ɗalibi ne a makarantar Gwamnati ta Gboko, kuma yana zaune a Makurdi tare da iyayensa
Makwabtan yankin Akpehe har yanzu suna mamakin yaron ya kashe kansa domin babu wanda zai iya sanin hakikanin abin da ya kai shi ga kashe kansa tun yana karami alhalin ya dogara ga iyayensa.”
Kokarin yin magana da mahaifin marigayin Mista Kula Tyochivir ya ci tura domin ya kadu matuka a sabili da afkuwar lamarin.
Da aka tuntuɓi Jami’ar hulɗar da jama’a na ‘yan sanda Sufeto Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin.
A wani labarin kuma:Rikici: Sama da mutane 81,000 ne suka shiga Habasha daga Sudan – Majalisar Dinkin Duniya
Rikici: Sama da mutane 81,000 ne suka shiga Habasha daga Sudan – Majalisar Dinkin Duniya
Adadin mutanen da suka isa Habasha sakamakon rikicin Sudan ya kai 81,095 a cewar hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya.
Ya zuwa ranar 16 ga watan Satumba, jimillar mutane 81,095 da ‘yan gudun hijira, da ‘yan cira ni da masu neman mafaka daga Sudan da ke fama da rikici suka shiga makwabciyarta, Habasha, in ji hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya, IOM.