A kalla mutane 6 Giwa ta kashe a kasar Zimbabwe, kawo yanzu a wannan shekarar, wanda hakan ya taimaka wajen kara haifar da rashin jituwa tsakanin dabbobin da kuma mutane.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar shine ya sanar da wannnan batu a yau Talata, ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Yanzu haka dai kasar Zimbabwe itace ta biyu a duniya dake da yawan Giwa, domin kuwa akwai Giwa 100,000 ta yanzu haka a kasar.
Kasar Bostwana itace ta farko a duniya dake da yawan giwaye, kuma kaso 1 bisa 3 na giwayen duniya sun kasance a yankin Africa.
Lamarin giwayen Zimbabwe ya zama wani na daban, sabanin a sauran wasu wurare da mutane ke hallaka Dabbobin, a kasar dabbobin ne ke hallaka mutanen, kuma yanzu haka yawa su ya karu da kaso biyar cikin 100.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce a shekarar 2021 giwaye sun kashe mutane 72.
Zimbabwe dai na da mutane miliyan 15, kuma suna karuwa a duk shekara da kaso 1.5.