Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika jajensa ga wadanda suka rasa rayukansu musamman wata Uwa da danta a sakamakon gobarar tanka da ya auku a garin Onitsha dake jihar Anambra.
Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce; shugaban kasar ya yi matukar kaduwa da shiga damuwa bisa yadda wannan uwa da danta suka rasa rayuwarsu sakamakon hatsarin tankar da ta kama da wuta.
Shugaban kasar har wala yau ya mika sakon jajensa ga wadanda gobarar ya shafa wanda ya hada da masu gidaje da kuma shaguna da sauran dukiyoyi da aka yi asara a yayin ibtila’in.